Business

Business and economy news

Gwamnatin Jigawa zata hada Kai da Qasar Brazil wajan Habaka Noman Ridi Da Qaro

Gwamnatin Jigawa zata hada Kai da Qasar Brazil wajan Habaka Noman Ridi Da Qaro

noman Qaro da Kuma yadda za a sarrafa Karon da yadda za,a sarrafa ridin Domin habaka tattalin A Nigeria . Yace nan gaba kadan Kungiyar manoman ta Kasa AFAN Zata ziyarci Qasar Brazil Domin tattaunawa dasu akan yadda za ahabaka harkokin noman a Najeriya . Yaci gabada cewar zasuyi iyaka bakin kokarinsu wajan inganta harkokin Manoma da inganta aikin noma a Jihar Jigawa . Yakuma nuna takaicinsa akan yadda harkokin noma suka karye,musamman a shekarar data gabata Kasancewar Manoma sun tafka hasara akan noma a shekarar data gabata. Yace Manoma da dama sun fuskanci matsalolin Rayuwa Masu yawa sakamakon yanayin da aka sami Kai aciki na tsadar taki da kayan noma. Sakamakon hakane yasa a wannan shekarar Gwamnati ta sake tunani akan yadda Zata taimakawa manoma Kuma ta habaka harkokin aikin Gona a fadin jihar ta jigawa. Engr Auwalu Ibrahim ya Bukaci Gwamnatin data tallafawa Manoma wajan baiwa manoman tallafin kayan noma Kai tsaye, Domin Ganin Manoman sun anfana . Ya Kuma shawarchi gwamnatin da ta rika baiwa manoman kayan noma Kai tsaye ta karkashin kungiyarsu ta Manoma a duk lokacin da Zata Bada tallafin kayan aikin gona. Yace akwai bukatar ace it'a gwamnatin ta sanyasu a cikin Domin sune suka San yayanta,Kuma idan lokacin yayi na amsar kaya sune zabi su amsowa Gwamnati kwayanta . Domin sauda yawa akan sami son zuciya wasu Yan siyasa sukan sanya siyasa wajan rabon kayan noman wadda ,hakan yasa akan sami akasi wajan yiwa harkokin noman zagon kasa a hana gwamnatin cimma manufarta da ta sanya a, gaba wajan Ganin ta inganta aikin Gona a fadin jihar ta jigawa dama Najeriya Baki daya . Yakuma bukaci Gwamnati ta hada Kai da Kungiyar Manoma Domin Ganin an ragewa manoman da sukayi hasara akan noma ,a shekarar data gabata. Yace yin hakan zai karawa manoman karfin gwiwa su maida hankali wajan inganta harkokin noman a Jihar Jigawa . Alh Auwal ya Kara da cewar Jihar Jigawa ta yi shuhura wajan inganta Harkar Noma ,haka yasa Jihar ta sami lambar yabo wajan Zama gwarzuwa a ɓangaren aikin Gona da Zaman lafiya . Saboda haka shugaban Qungiyar Manoman ta AFAN ya yabawa Gwamnatin Jihar ta Jigawa wajan cigaban Manoma.a Nigeria

Umar Akilu Majeri Feb 03, 2026