YA ZAMO WAJIBI MUSULMI SU GYARA TSARIN SIYASAR SU KAFIN ZABEN 2027
In Ji Dr. Abdurrahman Ibrahim IdrisĀ
Daga Muazu Hardawa BauchiĀ
An shawarci Yan arewacin Nigeria masu rike da masu rike da madafun iko musamman yan majalisun tarayya su inganta tunanin su.game da halin da Nigeria ke ciki kafin lokacin da za a gudanar da zaben kasa na shekarar 2027.
Sheikh Dr. Abdurrahman Ibrahim Idris malamin addinin musulunci a jihar Bauchi kuma shugaban kwamitin wayar da kan matasan musulmi game da yadda za a gyara makomar Nigeria shine ya bayyana haka a lokacin zaman musamman da ya yi da matasan musulmi a Bauchi.
Dr. Abdurrahman Ibrahim Idris ya bayyana cewa akwai bukatar a gyara tunanin mutane game da halin da kasa ke ciki don wayar da kan mutane musamman wajen samun Yan takara na gari don fiskantar siyasa da zabuka masu zuwa.
Yace akwai bukatar a ilmantar da mutane kan yadda za su gyara kan su ta hanyar dogaro da kai saboda mutane su fita daga halin rayuwar hannu baka hannu kwarya.
Musamman a wannan lokacin dole a kwadaitar da mutane game da yadda za su inganta sana'a don dogaro da kai saboda arziki ya zaina a hannun mutane.kowa ya samu hanyar ciyar da bakinsa.
Yace lokaci yayi da ya kamata matasan musulmi su sake tunani wajen neman mutane da za su gyara kasa musamman malamai da za su taimaka a samu gyara kasa ta hanyar fitowa don yin takara a madafun iko daban daban.
Ko kuma samar da yan takara Nagari da za su iya samar da gyara a siyasance da zamantakewa musamman ganin yawan mutane musulmi a Nigeria ya kai yadda za su iya fito fa Yan takara nagari da za su samar da jagoranci na gari.
Zaman ya tattauna kan yadda a wasu lokuta ake sa mutane a takarar siyasa amma idan sun kai ga nasara sai su watsar.da mutanen da suka zabo su.
Don haka aka bukaci samar da mutane masu alkibla da suka san mutunci mutane yadda idan an zabe su.baza su karya alkawarin da suka dauka a fiskar taimakon mutane ba.
Don haka aka bukaci dukkan musulmi su tsaya da adduah tare da wayar da kan mutane game da muhimmancin shiga siyasa don samar da shugabanni na gari.da za su taimaki mutane don a samu fita daga matsalar tsaro da tattalin arziki a ci gaba da gina kasa mai dorewa da kowa zai yi alfahari da ita.
No comments yet. Be the first to comment!