Opinion

NSCDC ta gano wata Masana’antar ƙera bindiga a Katsina

Mai Magana da yawun Rundunar tsaron, SC Buhari Hamisu ya shaidawa manema labarai haka a Katsina

UM

Umar Akilu Majeri

@Majeri

February 28, 2026 at 1:23 PM 65 views 0 comments
Share:
NSCDC ta gano wata Masana’antar ƙera bindiga a Katsina

NSCDC ta gano wata Masana’antar ƙera bindiga a Katsina


Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Mai Magana da yawun Rundunar tsaron, SC Buhari Hamisu ya shaidawa manema labarai haka a Katsina.

Ya ce jami’an tsaron sun gano wannan haramtacciyar masana’anta a ƙauyen kore da ke ƙaramar hukumar Ɓatagarawa bayan da suka sami sirri na maɓoyar miyagun mutanen.

SC Buhari ya sanar da cewa jami’an sun lalata wurin tare da kama mutane huɗu da kuma gano bindigogi, albarusai da wasu kayan ƙere ƙere.

Waɗanda aka kama sun haɗa da Haruna Lawal ɗan shekara 28 da Hamza Lawal mai shekaru 33 sai Badamasi Kabiru shekara 50 da Sagir Abba ɗan shekara 25.

Nan take da jami’an tsaron suka lalata masana’antar tare da ƙwace bindigogin da sauran kayan da suka ƙera.

Kayan da suka gano waɗanda ana zargin a masana’antar ake ƙera sun haɗa da bindigogi guda 8 da albarusai.

Sauran kayan sun haɗa da zargi,injin Gas, babura guda biyu diga da sauran su.

SC Buhari ya bayyana cewa rundunar tsaron za su cigaba da bincike domin gano inda suke saida waɗannan makamai da sauran ƙarin bayanai.

Ya jaddada ƙudirin rundunar tsaron na farin kaya ƙarƙashin kwamanda Abbas Dan Ale Maroki na ganin ta kare muhimman kayayyakin gwamnatin tarayya da samar da tsaro a jihar Katsina.

Ya buƙaci al’ummar jihar da su ba rundunar goyon baya ta bada bayanan sirri na inda maɓoyar miyagun mutane suke.

Media Gallery

<br />
<b>Deprecated</b>:  htmlspecialchars(): Passing null to parameter #1 ($string) of type string is deprecated in <b>/home/mizanine/public_html/public/article.php</b> on line <b>468</b><br />
Topics: #Opinion

Comments (0)

Leave a Comment

No comments yet. Be the first to comment!